Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya

'Yan tawaye sun hana bude kashi 14 na rumfunan zaben Afrika ta tsakiya

Hukumar Zaben Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ta bayyana yadda aka gaza gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a kashi 14 cikin 100 na mazabun kasar ranar Lahadin da ta gabata, sakamakon yadda kungiyoyin ‘yan tawaye masu dauke da makamai suka farwa masu kada kuri’a wanda ya tilasta kulle rumfunan.

Wasu jami'an zaben Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.
Wasu jami'an zaben Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya. AFP
Talla

Wani babban jami’I a hukumar zaben Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar Theopile Momokuama yayin zantawarsa da manema labarai a birnin Bangui ya ce ba a iya kada kuri’a a rumfunan zabe 800 cikin dubu 5 da 408 da ake da su a sassan kasar ba.

Rahotanni sun ce an iya gudanar da zaben na ranar lahadi ne kadau a babban birnin kasar Bangui da kuma wasu yankunan da ke karkashin kulawar sojojin Majalisar Dinkin Duniya.

Wasu alkaluma sun nuna cewa sama da masu kada kuri’u miliyan guda da dubu dari 8 suka gaza zuwa rumfunan zaben saboda fargabar tashin hankali tsakanin ‘yan tawaye da dakarun gwamnati.

Shugaba Faustin-Archange Touadéra dake neman wa’adi na biyu, ya zargi magabacinsa, tsohon shugaban kasa François Bozizé, da kitsa juyin mulki ta hanyar marawa kungiyoyin ‘yan tawaye baya.

Sai dai Bozizé, wanda aka hana shi takara kuma ya ke karkashin takunkumin Majalisar Dinkin Duniya ya musanta ikirarin na gwamnati.

Kungiyoyin ‘yan tawayen wadanda suka kwace garuruwa da dama da ke kusa da Bangui babban birnin kasar, sun yi kira ga al’umma da su kauracewa zaben.

Yayin da gwamnatin ta yi watsi da kiran da ‘yan adawa suka yi na a dage zaben saboda rashin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.