Isa ga babban shafi
Afrika

Zancen dage zaben bai taso ba a Afrika ta Tsakiya- Kotu

Kotun fasalta kudin tsarin mulkin Jamhuriyar tsakiyar Afrika ta yi watsi da daukaka kara da jagoran yan adawa suka shigar dangane da zaben da zai guda a gobe lahadi.Yan siyasar sun bukaci a dage zaben shugaban kasar,sai dai alkalan kotun sun ce zancen dage zaben bai taso ba.

Faustin-Archange Touadéra, Shugaban Jamhuriyar Tsakiyar Afrika
Faustin-Archange Touadéra, Shugaban Jamhuriyar Tsakiyar Afrika RFI/Romain Ferré
Talla

A dai- dai lokacin da kotun fasalta kudin tsarin mulkin kasar ke soke bukatar yan adawa,kasashen Duniya na ci gaba da bayyana damuwa tareda yin Allah wadai da kisan dakarun wanzar da zaman lafiya yan kasar Burundi da yan tawaye suka hallaka.

Rahotanni daga kasar na nuni cewa sojoji tareda hadin gwuiwar dakarun wanzar da zaman lafiya na cigaba da sa ido kan manyan hanyoyin shiga babban birnin kasar Bangui a jajuburin zaben shugaban kasar.

Sojojin Burundi dake aiki wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika uku ne yan tawaye suka kashe a Dekoa dake tsakiyar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika.

Kisan sojojin na zuwa ne a wani lokaci da yan tawaye suka sanar da yi watsi da duk wata yarjejeniyar sulhu ko tsaigaita wuta tareda bukatar gwamnati ta dage zaben Shugaban kasar na gobe lahadi.

Shugaban kasar Faustin Archange Touadera a yayin yakin neman zabe y ace babu ta yada za a dage wannan zabe,ya kuma yi amfani da wannan dama ,inda ya dinga gayatar jama’a da su fito ranar zabe.

Majalisar Dimkin Duniya ta dai Allah wadai da kisan dakarun ta da ake zargin yan tawaye da aikatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.