Kotun Bangui ta yi watsi da takarar Francois Bozize
Kotun Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta yi watsi da bukatar takarar tsohon shugaban kasa Francois Bozize a zaben shugabancin kasar mai zuwa sakamakon tuhumarsa da aikata kisa da azabtar da mutane da kuma takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakkaba masa.
Wallafawa ranar:
Kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar ta gabatar da wannan hukumci ne, bayan da alkalan kotun suka sanar da soke takarar wasu karin yan takara 3 a zaben da zai gudana ranar 27 ga watan nan.
A watan Satumba na shekarar 2020 ne tsofin shugabanin kasashen Afrika ta tsakiya, Francois Bozize da Michel Djotodiya suka samu ganawa a babban birnin kasar Bangui.
Tsohon Shugaban kasar Michel Djotodiya musulmi na farko da ya shugabanci kasar ya dawo gida bayan da ya share kusan shekaru shida ya na gudun hijira a Jamhuriyar Benin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu