Isa ga babban shafi

Tsohon shugaban Afrika ta Tsakiya ya marawa 'yan tawaye baya

Tsohon shugaban Afrika ta Tsakiya Francois Bozize da kotu da haramta mishi tsayawa takara, ya bukaci daukacin ‘yan kasar da su kauracewa zaben da ya gudana na shugaban kasa da na ‘yan majalisa.

Tsohon shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Francois Bozize
Tsohon shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Francois Bozize Simon Maina/AFP
Talla

Cikin wani sakon murya da aka wallafa a shafukan intanet, Bozize ya bayyana goyon bayansa gamayyar kungiyoyin ‘yan tawayen kasar ta CPC, da suka sha alwashin kawar da gwamnatin Faustin Archange Touadera.

Yau lahadi ne dai al’ummar Afrika ta tsakiyan suka kada kuri'unsu a zaben shugabancin kasar, da na ‘yan majalisu, inda shugaba Touadera ke neman wa’adi na 2.

Zaben yazo a yayin da sojojin kasar ke cigaba da fafatawa da ‘yan tawayen da suka sha alwashin hana gudanarsa, bayan janye shelar tsagaita wutar da suka yi, gami da kudurar aniyar kame Bangui, babban birnin kasar.

Kafin karkare zaben dai rundunar dakarun Majalisar Dinkin Duniya dake aikin wanzar da zaman lafiya a Afrika ta Tsakiyan ta MINUSMA ta ce wani gungun 'yan tawaye ya afkawa garin Bria da harbe-harbe, abinda ya tilastawa jama'a tsrewa da rumfunan zabe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.