Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya

Rikici ya tilastawa mutane fiye da dubu 30 tserewa daga Afrika ta tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan yadda rikicin Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ya tilastawa mutane fiye da dubu 30 ficewa daga kasar yayinda wasu dubbai kuma yanzu haka rikicin ya raba su da muhallansu a sassan kasar

Wasu da rikici ya raba da muhallansu a Bangui babban birnin Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.
Wasu da rikici ya raba da muhallansu a Bangui babban birnin Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya. AFP PHOTO / FRED DUFOUR
Talla

Hukumar kula da ‘yan cirani ta Majalisar UNHCR ta ce ‘yan gudun hijrar jamhuriyyar Afrika ta tsakiyan da suka tsallake kasar don gujewa rikicin yanzu haka na cikin matsananciyar bukatar agajin gaggawa.

Alkaluman da UNHCR ta fitar ya nuna cewa akwai ‘yan gudun hijirar Afrika ta tsakiyan fiye da dubu 24 a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo yayinda wasu dubu 4 da 500 ke Kamaru kana wasu mutum dubu 2 da 200 a Chad baya ga kusan 70 a Congo.

Mai magana da yawun hukumar Boris Cheshirkov ya shaidawa manema labarai a Geneva cewa ficewar mutanen fiye da dubu 30 daga Afrika ta tsakiya bisa tilascin sakamakon tabarbarewar tsaro a yankunansu na da alaka da zaben kasar na ranar 27 ga watan Disamba.

Mr Boris ya ci gaba da cewa mutane dubu 185 daga yankunan kasar 25 yanzu haka sun bar matsugunansu ta yadda wasun su ke ci gaba da rayuwa a dazuka tun daga ranar 15 ga watan Disamban bara zuwa yanzu.

Sai dai a cewar kakakin na UNHCR akwai mutane dubu 62 wadanda suka samu sukunin iya komawa matsugunansu ko da yake su kansu na fuskantar mummunar barazana da ke neman tilasta musu sake kauracewa gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.