Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya

Yawan 'yan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dake gudun hijira ya ninka cikin mako 1

Majalisar dinkin duniya tace adadin ‘yan gudun hijirar dake tserewa hare-haren ‘yan tawaye a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, ya ninka daga dubu 30 zuwa 60 a mako daya.

Wasu 'yan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dake gudun hijira a Kamaru, yayin da suka yi layi don karbar tallafin abinci.
Wasu 'yan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dake gudun hijira a Kamaru, yayin da suka yi layi don karbar tallafin abinci. UNHCR / C. TIJERINA
Talla

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya UNHCR tace sama da mutane dubu 50 da suka tsere daga Afrika ta Tsakiyan sun tsallaka cikin Jamhuriyar Congo, daga cikinsu kuma 10 sun isa kasar ne a ranar Laraba kadai, bayan da ‘yan tawayen suka sake yunkurin afkawa birnin Bangui.

Yayin ganawa da manema labarai a birnin Geneva, kakakin hukumar ta UNHCR Boris Cheshirkov, ya ce baya ga dubban ‘yan gudun hijirar dake Jamhuriyar Congo, akwai wasu ‘yan Afrika ta Tsakiyan akalla dubu 58 dake gudun hijira a sansanonin cikin gida, yayin da wasu dubu 9 suka tsere zuwa Kamaru.

Akalla dala miliyan 151 majalisar dinkin duniya ke nema don tallafawa wadanda suka tagayyara a dalilin hare-haren ‘yan tawaye a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Ranar 4 ga watan Janairun nan hukumar zaben kasar ta sanar da shugaba mai ci Faustin Archange Touadera a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gudana na 27 ga watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.