Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Dakarun Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun halaka 'yan tawaye 44

Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tace dakarun ta sun yi nasarar kashe Yan tawaye 44 lokacin da suka yiwa birnin Bangui kawanya da zummar kifar da gwamnatin shugaba Archange Touadera. 

Dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya REUTERS/Antoine Rolland
Talla

Sanarwar gwamnatin yace dakarun kasar tare da hadin kan na kawance sun kaddamar da hare hare a kauyen Boyali dake da nisar kilomita 90 daga Bangui inda suka kashe maharan, ba tare da samun matsala daga bangaren dakarun su ba.

Gwamnatin kasar tace cikin wadanda aka kashe harda sojojin haya daga Chadi da Sudan da kuma Yan kabilar Fulani.

A makon jiya, majalisar dinkin duniya tace adadin ‘yan gudun hijirar dake tserewa hare-haren ‘yan tawaye a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, ya ninka daga dubu 30 zuwa 60 a mako daya.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya UNHCR tace sama da mutane dubu 50 da suka tsere daga Afrika ta Tsakiyan sun tsallaka cikin Jamhuriyar Congo, daga cikinsu kuma 10 sun isa kasar ne a ranar Laraba kadai, bayan da ‘yan tawayen suka sake yunkurin afkawa birnin Bangui.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.