Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya ta fara bincike kan cin zarafin fararen hula

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ce ta fara gudanar da bincike kan rahotannin kashe fararen hula da dama da ake zargin sojojin kasar da kuma sojojin hayar wani kamfanin tsaron Rasha da aikatawa.

Wasu sojojin hayar Rasha na kamfani Wagner a wani yankin na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, watan Disambar 2021.
Wasu sojojin hayar Rasha na kamfani Wagner a wani yankin na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, watan Disambar 2021. © Observateur civil anonyme
Talla

A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu, sojoji da abokan kawancen su, sun kai hari a kauyukan Gordil da Ndah, da ke arewa maso gabashin birnin Bangui, wanda ya yi sanadiyar kashe fararen hula.

Babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin bil'adama, Michelle Bachelet, ta yi Allah wadai da take hakkin bil'adama da aka yi a kasar, da suka hada da kashe ‘yan ba ruwan mu da cin zarafin mata, da kungiyoyin 'yan tawaye da kuma sojojin kasar da kawayensu na Rasha ke aikatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.