Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

An kori sojojin Afrika ta Tsakiya 80 daga aiki

Mahukumtan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, sun kori  sama da sojoji 80 daga bakin aiki, sakamakon zargin su da aikata laifuka da suka hada cin zarafi, tursasa wa jama’a tare da kafa shingaye ba kan ka’ida ba.

Wasu sojojin Afrika ta Tsakiya
Wasu sojojin Afrika ta Tsakiya AFP/Desirey Minkoh
Talla

'Yan kasar sun jima suna kokawa kan yadda sojoji ke cin zarafin farraren hula tare da hadin bakin wasu dakarun haya na kasar Rasha.

Yayin da wasu kafofin yada labaren kasar ke kallon wannan mataki a matsayin farfaganda, fadar shugaban kasar ta bakin kakkakinta Albert Yoloke Mokopme ta ce daukar wannan mataki tamkar saka da’a a cikin rundunar sojin Afrika ta tsakiya.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da hukumomin kasar suka dauki irin wannan mataki ba domin a shekara ta 2021, hukumomin sun dauki matakin sallamar wasu daga cikin sojojin  kasar, matakin da jama’a suka yaba a kai.

Wasu bayanan baya-baya-nan na nuni cewa, daga cikin sojojin 80 da aka kora daga aiki, bakwai daga cikinsu  an same da laifin tursasa wa jama’a tareda kafa shingaye ba bisa ka’ida ba.

Mashar’anta na hasashen cewa mudin hukumomin wannan kasa ba su dauki mataki da ya dace  tare da sa ido kan wadanan sojoji da suka kora daga aiki, Paul Crescent Beninga,wani dan rajin kare hakokkin bil Adam ya na mai bayyana  cewa wadanan sojojin da aka kora daga aiki za su iya canza tunani zuwa kama aiki tareda yan tawaye,sabili da haka a cewarsa ya zama tilas gwamnati ta nuna ba sani ba sabo a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.