Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

MDD na bincika zargin sojin Afirka ta Tsakiya da na Rasha kan kisan fararen hula

Majalisar Dinkin Duniya na gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma sojojin hayar Rasha na kamfanin Wagner, ka yi wa mutane da dama kisan gilla a makon da ya gabata.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, yayin ziyarar Paparoma Francis, 10 ga Nuwamba, 2015.
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, yayin ziyarar Paparoma Francis, 10 ga Nuwamba, 2015. REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Sama da fararen hula 30 ne aka kashe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyan, a wani harin da aka kai a kusa da garin Bria tsakanin 16 zuwa 17 ga watan Janairu, farmakin da aka yi nufin aiwa kungiyar ‘yan tawayen Union for Peace, a cewar daya daga cikin majiyoyin da suka nemi a sakaya su.

A halin da ake ciki, rundunar MINUSCA ta dakarun wanzar da zaman lafiyar Majalisar Dinkin Duniya na kokarin tuntubar wadanda suka tsira daga harin, domin tantance gaskiyar lamarin.

Sai dai har yanzu sashin sadarwa na Majalisar Dinkin Duniya ya ki cewa komai kan lamarin

A tsakiyar shekarar bara ta 2021, kwararrun Majalisar Dinkin Duniya da aka tura zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, suka bayyana damuwa kan rahotannin munin yanayin take hakkin dan Adam a kasar, da ake zargin sojojin haya na Rasha da aikatawa, wadanda aka baiwa kwangilar tallafawa sojojin gwamnatin Afrika ta Tsakiyan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.