Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

'Yan tawaye sun hallaka mutane 32 a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Hukumomin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun ce mutane 32 'yan tawaye suka hallaka a karshen mako, cikin su har da sojoji guda 2 a ci gaba da tashin hankalin da ake samu a kasar.

Wani yanki na birnin Bangui.
Wani yanki na birnin Bangui. REUTERS/Alain Amontchi
Talla

Jami’in mulkin yankin da aka kai harin da ke iyaka da kasar Kamaru, Esaie Gbanin ya ce an kaddamar da hare haren guda biyu ne a kauyukan Kaita da Bayengou mai nisan kilomita 500 daga Bangui babban birnin Kasar

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fada cikin tashin hankali tun bayan kifar da gwamnatin Francois Bozize, wanda ya kai ga daukar makaman 'yan tawaye don kalubalantar gwamnati da ke ci.

Yanzu haka dai akwai sojojin Rasha da na Angola na cikin wadanda ke taimakawa kasar yaki fa 'yan tawayen wadanda ke ci gaba da zafafa hare-hare a kauyukan kan iyaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.