Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai-Afirka ta Tsakiya

Turai ta dakatar da horar da dakarun Afirka ta tsakiya saboda sojin hayar Rasha

A wani mataki na wucin gadi Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana dakatar da horon da take bai wa dakarun sojin kasar jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, sakamakon aikin tsaron da sojojin hayar kamfanin Wagner na kasar Rasha ke yi  a kasar,  kamar yadda tawagar kungiyar Tarayyar Turan dake Bangui ta sanar.

Tarayyar Turai ta nuna rashin amincewa da dauko sojin haya daga Rasha.
Tarayyar Turai ta nuna rashin amincewa da dauko sojin haya daga Rasha. © YVES HERMAN/REUTERS
Talla

Sakamakon horon tsaro da sojojin hayar na kamfanin na Wagner ke baiwa dakarun tsaron kasar jamhuriyar Afrika ta tsakkiya (FACA), ne kungiyar Tarayyar Turai ta nuna damuwarta kan batun da ya shafi mutunta yancin gudanar da  ayukan agajin kasashen duniya ne, ta yanke shawarar wucin gadin dakatar da ayukan da take gudanarwa na baiwa sojojin kasar horo.

Kamar yadda babban komandan dakarun Turai a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Janar Jacques Langlade de Montgros, ya sanar wa kamfanin dillancin labaran Faransa.

 Janar Montgros ya ci gaba da cewa, sojojin hayar na bai wa dakarun kasar ta JAT horo, da kuma da ayukan tsaro ne  ya sa kungiyar ta turai ta dakatar da nata horon da take baiwa sojojin kasar na wucin gadi

sai dai kungiyar ta turai ta ce, horon da take baiwa rundunar sojin na JAT zai iya ci gaba,  matsawar ta samu tabbacin cewa,  sojojin JAT da ta horar  ba za su yi aiki tare da sojojin sa kai na Wagner"ba.

Yanzu haka dai tuni kimanin masu bada horon kungiyar tarayyar turan 70 ne suka koma kasashensu na asali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.