Isa ga babban shafi
MDD-Rasha

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Rasha da yi mata zagon kasa

Jami'an diflomasiyya sun zargi Rasha da dakile ayyukan kwamitocinsu da ke sanya ido kan mutunta takunkuman haramta cinikin makamai da na tattalin arziki da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa wasu yankunan ko kasashen masu fama da rikici ciki har da Mali.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. POOL GETTY IMAGES NORTH AMERICA/AFP/File
Talla

Jami'an Diflomasiyyar kwamitocin na Majalisar, sun ce yankunan da ake kakabawa takunkumai saboda mabanbantan dalilai na samun goyon bayan Rasha ta karkashin kasa, lamarin da Majalisar ta bayyana da yunkurin zagon kasa ga lamurranta.

Ikirarin Majalisar na zuwa a dai-dai lokacin da Rashan ke ci gaba da yunkurin fadada ayyukan ta a kasashen Afirka ciki har da kasashen da ke matsayin renon Faransa, yankunan da har zuwa yanzu su ke karkashin ikon uwar goyon na su ta mulkin mallaka.

Majalisar Dikin Duniya ta kuma zargi Rashan da kin bayar da hadin kan da ya kamata cikin kwamitocinta a lamurran da suka shafi zaman lafiyar Duniya da kuma dakile yunkurin tayar da zaune tsaye.

A cewar Majalisar ta bakin jami'an Diflomasiyyar kwamitocin Rasha na yin jan kafa wajen taimakawa don tabbatar da takunkumin da aka sanyawa Jamhuriyar Africa ta tsakiya da kuma Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, har wa’adin da aka dibar musu ya kare.

Majalisar ta gwada misali da yadda wa’adin takunkumin da aka sanyawa kasashen Sudan da Mali ya kare, ba kuma tare da Rashan ta bayar da hadin kan da ya kamata wajen zaman tattaunawa kan batun ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.