Isa ga babban shafi
Somalia

Kwamitin sulhu na MDD ya nemi sansanta rikicin siyasar Somalia

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwa kan rikicin da ke ta'azzara tsakanin shugaban Somalia da Firaministan sa, inda ya yi kira ga jagororin su kai zuciya nesa tare da shiga tattaunawar sulhu.

Shugaban Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed Farmajo, da Firaminista Mohamed Hussein Roble.
Shugaban Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed Farmajo, da Firaminista Mohamed Hussein Roble. © Caasimada Online
Talla

Rikicin da ya dade yana ta'azzara tsakanin shugabannin biyu ya karu ne a wannan makon, lokacin da shugaba Mohammed Abdullahi Mohammed, wanda aka fi sani da Farmajo, ya dakatar da ikon zartaswar Firaminista Mohamed Hussein Roble, matakin da Firaministan ya yi watsi da shi.

Mutanen biyu na rikici ne kan rabon wasu manyan mukamai, rashin jituwar da ke barazana ga shirin zaben kasar ta Somalia da kuma tunkarar mayakan Al Shebaab.

Cikin watan Mayu, ‘yan majalisar dokokin Somalia suka kada kuri’ar soke karin wa’adin shugabanci na shekaru biyu da suka amince da shi a watan da ya gabata, sakamakon kazamin rikici da ya barke a Mogadishu babban birnin kasar tsakanin bangarorin jami’an tsaro, wadanda suka samu rarrabuwar kawuna kan batun.

A jawabin da ya gabatar bayan kada kuri'a a majalisar dokoki, Firaminista Mohamed Hussein Roble ya umarci sojojin da su koma bariki sannan ya bukaci 'yan siyasa su guji tayar da rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.