Babu wata fa'ida dangane da baiwa Taliban damar magana a zauren MDD - Jamus
Kasar Jamus ta ce babu wata fa’ida cikin baiwa kungiyar Taliban damar halartar taron majalisar dinkin duniya karo na 76.
Wallafawa ranar:
Ministan harkokin wajen kasar ta Jamus Heiko Maas ya ce abin takaici ne ma yadda aka baiwa Taliban damar magana har ma ta bukaci a ba ta damar gabatar da jawabi.
A cewar Maas, duk wani jawabi da Taliban din za ta yi wa jama’a bashi da wata Fa’ida, matukar ba za su yi biyayya ga dokokin kasa da kasa da kuma cika alkawurran da suka dauka.
A cewar Ministan, hatta halartar Taron da Taliban din ta yi ma bashi da wani muhimmanci, a don haka bai kamata a basu damar yin wani jawabi ba, har sai an ga sun fara daukar matakai ba wai zancen fatar baki ba.
Idan dai za’a iya tunawa Taliban ta fara fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya tun lokacin da ta sake karbe iko da gwamnatin kasar a cikin watan Agustan da ya gabata.
Wannan ta sa kasashen duniya ke bayyana fargaba a game da makomar hakkin dan adam a kasar da kuma yadda Taliban din ta fara karya alkawurran da ta dauka na kare hakkin mata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu