Isa ga babban shafi
Afrika-Balaka

Tsohon jagoran 'yan tawayen Anti Balaka ya gurfana gaban ICC

A karon farko tsohon jagoran ‘yan tawayen Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da ake zargi da aikata laifukan yaki da kuma ta ke hakkin bil-Adama Maxime Makom, ya bayyana a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.

 Wannan ne karon farkon da jagoran 'yan tawayen na Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ke bayyana a gaban kotu.
Wannan ne karon farkon da jagoran 'yan tawayen na Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ke bayyana a gaban kotu. © Gaël Grilhot/RFI
Talla

Tsohon jagoran kungiyar ‘yan tawayen na Balaka, ana zargin sa ne da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil-Adama a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2014 a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Makom mai shekaru 43, a ranar Litinin ne Chadi ta mika shi ga hukumomin kotun ta ICC da ke birnin Hague a Holland, inda ya tabbatar da cewar an shaida masa lafukan da ake zargin sa da aikatawa.

Lauyan sa ya bayyana cewar, hukumomin Chadi sun azabtar da Makom a tsawon lokacin da ya shafe a hannunsu ta yadda suka rika ciyar da shi lalataccen burodi baya ga barinsa ya kwana a kasa ba gado.

An dai tsaida ranar 31 ga watan Janairun badi domin fara sauraron karar.

Rikicin da ‘yan tawayen Seleka da kuma Balaka suka haifar a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma sanya wasu rasa muhallan su.

Tuni dai aka gurfanar da biyu daga cikin wadanda suka jagoranci tawaye a kasar, Patrice Edouard Ngaissona da kuma Alfred Yekatom a gaban kotun, yayinda aka tsaida watan Satumba don fara shari’ar Mahamat Said Abdel Kani wanda ake zargi a matsayin kwamandan kungiyar Saleka da aikata laifukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.