Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya na bincike kan kisan fararen hula a Afrika ta tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da bincike kan kisan gillar da aka aikata a garin Bria, mai tazarar kilomita  600 gabashin Bangui babban birnin jamhuriyar Afrika ta tsakkiya.

Wani yanki na Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.
Wani yanki na Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya. AFP/File
Talla

Harin hadin guiwar dakarun gwamnati da na sojin hanyar kasar rasha na kamfanin tsaro Wagner da aka kai a ranaku 16 da 17 ga wannan wata na jairu  ya yi sanadiyar mutuwar gomman fararen hula.  

Wata majiyar Majalisar da ta bukaci sakaya sunanta ta sanar da cewa dakarun hadin guiwar sun kai harin ne da zummar fatatakar dakarun babbar kungiyar yan tawayen (UPC), dake da karfi a yankin gabashin kasar,.

Sama da fararen hula 30 ne aka kashe wasu daga cikinsu ta hanyar kuskureren harsashen bindiga tare da bayyana kwasar ganima daga maharan.

Dakarun gwamnatin jamhuriyar Afrika ta Tsakkiya da na sojin hayar Rasha sun aikata kisan kiyashi kamar yadda wata majiyar sojin gwamnati da ta bilaci sakaya sunanta  ta sanar da kamafanin dillancin labaran  l'AFP.  Inda ta ci gaba da cewa sun gudanar da kisan bai daya ne akan mutane sama da 50.

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a jamhuriyar Afrika ta tsakkiya (Minusca) ta fara gudanar da yiwa jama’a tambayoyi domin tabbatar da haske kan abinda ya faru a cewar wata majiyar majalisar ta dinkin duniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.