Birnannun nakiyoyi na barazana ga ayyukan jinkai a Afrika ta tsakiya
A Jamhuriyar Tsakiyar Afrika, kungiyoyin agaji na ci gaba da bayyana damuwa ganin ta yada wasu yankunan kasar da ke da arzikin ma’adinai ke tattare da hatsari ga kungiyoyin agajin, kasancewa yan tawaye sun dasa nakiyoyi a yankunan.
Wallafawa ranar:
Yankin Arewa maso yammacin Afrika ta tsakiya ya kasance yankin mai tattare da hatsari ga kungiyoyi masu aikin jin kai dama direbbobin sufuri dake rayuwa cikin kutsi inda ake kyautata zaton kungiyoyi dauke da makamai sun dasa nakiyoyi saman wadanan hanyoyi..
A farkon shekarar nan ta 2022 daya daga cikin wakilan yan atchaba mai suna Lagos Yandja dake aiki a wannan yankin ya sheidawa kamfanin dilancin labaren faransa cewa saman hanyar Paoua dake da nisan kilometa 500 da babban birnin kasar Bangui, an samu mutuwar daya daga cikin yan atchaba da ya taka nakiya ya kuma rasa ran sa nan take, ya karasa da cewa aikin na su na tattare da hatsari, a na sa geffen Augustin Ndusha dake aiki da wata kungiyar agaji,ya na tunai da irin ta’asar da nakiya ta yiwa motar da yake cikin ta.
Hukumomin kasar sun yi shelar cewa yanzu kam sun kwace wasu yankuna daga hannun kungiyoyi masu dauke da makamai, yayinda a zahiri dakarun gwamnati ke fuskantar turjiyya mai karfi daga wadanan kungiyoyi da za mu iya zana yan tawayen 3R, daya daga cikin manyan kungiyoyin yan tawayen Afrika ta Tsakiya da suka dasa nakiyoyi da dama a wadanan yankuna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu