Isa ga babban shafi

Rasha ta gayyaci jakadan Faransa bayan harin da aka kaiwa sojojin Wagner

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta gayyaci jakadan Faransa a birnin Moscow, biyo bayan sakon wani kunshi da ke dauke da bam wanda aka aikawa jami’an kamfanin sojin haya Wagner da ke birnin Bangui Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Wasu sojojin Wagner kenan
Wasu sojojin Wagner kenan AFP - OLGA MALTSEVA
Talla

Bayan faruwar wannan lamari,  Rasha ta yi zargin cewa Faransa tana da hannu a harin, zargin da tuni mahukuntan birnin Paris suka yi watsi da shi.

Moscow ta fada a makon da ya gabata cewa daya daga cikin wakilanta a kasar Afirka ya samu rauni sakamakon fashewar wani abu.

Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna ta yi watsi da ikirarin da shugaban kamfani Wagner na Rasha, Yevgeny Prigozhin, ya yi na cewa gwamnatin Paris na da hannu, kuma ya kamata a ayyana Faransa a matsayin kasa mai daukar nauyin ta'addanci, inda ta bayyana ikirarin a matsayin farfagandar Rasha.

Rasha ta tabbatar da cewa ta gayyaci jakadan Faransa a Rasha Pierre Levy da wanda ya gabatar da korafi a hukumance kan kalaman da ba su dace ba.

Dakarun Faransa na karshe da aka tura Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun bar kasar a makon da ya gabata bayan dambarwar dangantakar mai karfi tsakanin Bangui da Moscow abin da ya sanya aka tura sojojin Wagner zuwa kasar domin murkushe masu dauke da makamai da suka addabi kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.