An gudanar da zanga-zangar adawa da sauya kundin mulki a Afirka ta Tsakiya
Daruruwan ‘yan kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ne suka bijirewa dokar hana fita jiya Jumma’a suka gudanar da zanga-zanga a birnin Bangui don nuna adawa da shirin sauya kundin tsarin mulkin kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gamayyar jam'iyyun adawa ta "Republican Bloc for the Defence of the constitution” ce ta shirya tattakin.
Babban sauyi dake cikin daftarin fasalta kundin tsarin mulkin dai zai bada dama shugaban kasa ya yi ta mulki har tsawon rayuwarsa, wanda zai kawo karshen wa'adi 2 da shugaban kasa ke yi a halin yanzu.
'Yan adawar sun jagoranci wani tattaki na kusan mutane 500 karkashin rakiyar jami'an tsaron kasar da motocin sulke da tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya MINUSCA ta girke, kamar yadda 'yan jaridar AFP suka shaida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu