Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

'Yan adawa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun yi watsi ta tattaunawar kasa

Gungun ‘yan adawar jamhuriyar Africa ta tsakiya sun bayyana janyewar su daga taron sulhuntawa da za’a gudanar a kasar, bayan da aka janye gayyatar da aka yiwa shugabannin ‘yan tawayen kasar.

Shugaban kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Fustin Archange Touadéra.
Shugaban kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Fustin Archange Touadéra. REUTERS/Sergei Karpukhin
Talla

Jamhuriyar Africa ta tsakiya dai ta fada cikin tashin hankali ne tun shekarar 2013, to amma a makon da ya gabata Shugaban kasar Faustin Archange Touadera ya bukaci tattaunawar sulhu da dukannin masu ruwa da tsaki makkonni 15 da ya shan alwashin yin wannan zama amma ban da ‘yan tawaye.

To amma dakatar da shugabannin ‘yan tawayen kasar daga halartar taron ne ya sanya kakakin gungun ‘yan adawar Nicolas Tiangaye ya sanar da kin halartar ta su a taron da aka shirya gudanar da shi wannan litinin.

Sai dai duk da wannan sanarwa Kakakin gwamnatin kasar Albert Yaloke Mokpeme ya ce za’a gudanar da taron, yana mai cewa shugaban kasar ya yi mamakin janyewar ‘yan adawar daga halartar taron.

Gudanar da taron hadin kan da tabbatar da zaman lafiya na cikin alkawurran da shugaban kasar ya dauka a yayin yakin neman zaben da ya gudanar a bara, a yunkurin sa na mayar da kasar kan wanzajjen zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.