Isa ga babban shafi

Al'ummar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya na kada kuri'a a zaben raba gargdama

Yau lahadi al’ummar jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ke kada kuri’ar raba gardama kan garambawul ga kundin tsarin mulkin kasar wanda idan har ya samu rinjayen kuri’un da ke goyon bayansa zai bayar da dama ga shugaba Faustin Archange Touadera ya sake neman wa’adin mulkin kasar a zaben da ke tafe.

Al'umma na kada kuri'ar garambawul ga kundin tsarin mulki a jamhuriyyar Afrika tya tsakiya.
Al'umma na kada kuri'ar garambawul ga kundin tsarin mulki a jamhuriyyar Afrika tya tsakiya. AFP - BARBARA DEBOUT
Talla

Tuni dai bangaren adawa da ke kalubalantar wannan kudiri, ya bukaci magoya bayansa da su kada kuri'ar kin amincewa da shi, wanda suka bayyana da wani salon wayo na ci gaba da zaman gwamnati mai ci a madafun iko.

Wasu rahotanni da safiyar yau lahadi sun nuna yadda aka samu fitar jama’a musamman a fadar gwamnatin kasar Bangui wadanda suka fito don kada kuri’a kan kudirin na garambawul, duk da cewa babu tabbacin su kasance masu goyon baya ko akasin haka.

Ko a juma’ar da ta gabata anga yadda mutane fiye da dubu 3 suka yi dafifi a birnin Bangui don nuna goyon baya ga shirin kada kuri’ar na yau lahadi duk kuwa da yadda bangaren adawa ke ci gaba da nuna rashin goyon baya.

Shugaban shirin garambawul ga kundin tsarin mulkin na jamhuriyyar Afrika ta tsakiya Evariste Ngamana ya bayyana kwarin gwiwar samun nasarar kudirin wanda zai mayar da wa’adin mulkin kasar zuwa shekaru 7 daga 5 da ake yi a yanzu haka.

Haka zalika idan har kudirin garambawul din ya samu nasarar sahalewar jama'ar kasar kenan dama ce da za ta janye shingen da ya haramta dorawa daga wa’adi 2 na mulkin kasar, lamarin da ke nuna shugaba guda zai iya yin wa'adin mulki iyakar karfinsa ba tare da shinge ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.