Isa ga babban shafi

Mummunar gobara ta jikkata mutane fiye da 80 a birnin Conakry

Akalla mutane 8 suka mutu, yayin da wasu 84 kuma suka jikkata sakamakon fashewar wani abu a wata tashar mai da ke Conakry babban birnin kasar Guinea a safiyar ranar Litinin din nan.

Yadda gobara ta tashi bayan fashewar wani abu a tashar da ake adana man fetur da ke tsakiyar Conakry, babban birnin kasar Guinea.
Yadda gobara ta tashi bayan fashewar wani abu a tashar da ake adana man fetur da ke tsakiyar Conakry, babban birnin kasar Guinea. © FRANCE 24
Talla

Jami’in Dan Sandan da ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce adadin da suka bayar na mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin fashewar na wucin gadi ne, la’akari da cewar akwai yiwuwar ya karu.

Bayanai sun ce gilasan tagogin gine-gine da dama da ke kusa da ma'adanar man sun fashe, yayin da daruruwan mutane suka tsere, sakamakon fashewar da aka samu a tashar man fetur din wadda ita ce irinta guda daya tilo a Guinea, da ke gundumar Kaloum a tsakiyar Conakry babban birnin kasar.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce ana iya hangen mummunar gobarar da tashi daga nisan kilomita akalla guda, yayin da jami'an kwana-kwana suka garzaya zuwa wurin, inda tuni wasu manyan motocin dako na tanka suka fice daga ma'ajiyar ta man fetur, tare da rakiyar sojoji da 'yan sanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.