Isa ga babban shafi

Gobara a tashar man fetur ta kashe mutane 34 a Jamhuriyar Benin

Akalla mutane 34 ne suka mutu bayan fashewar da ta faru a wani depon man fetur da ke yankin Seme Podji a kudancin Jamhuriyyar Benin, lamarin da ya haddasa mummunar gobara da ta kone tarin motoci wasun su dauke da fasinja.

Baya ga mutane 34 da suka mutu akwai kuma wasu 20 da suka samu muggan raunuka.
Baya ga mutane 34 da suka mutu akwai kuma wasu 20 da suka samu muggan raunuka. via REUTERS - STATE EMERGENCY SERVICES OF UKRA
Talla

Majiyar labarai daga yankin da ibtila’in ya faru sun bayyana cewa zuwa safiyar ranar Lahadi an tabbatar da dauko gawarwakin mutane 34 yayin da wasu da dama suka jikkata baya ga asarar dimbin dukiya.

Rahotanni sun bayyana cewa yankin da fashewar ta faru wuri ne da galibi masu ababen hawa na haya da suka kunshi motoci, babura masu kafa biyu da masu kafa uku kan yi dandazo ko dai don shan mai ko kuma hada-hadarsu ta yau da kullum.

A cewar rahotanni galibin man da ake shiga da shi Benin daga Najeriya ta barauniyar hanya akan yi hada-hadarsa ne a tashar man fetur da ke Seme Podji, duk da yadda gwamnati ta haramta hada-hadar man na sata.

Ministan cikin gida na Benin Alassane Seidou, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar duk da cewa bai yi cikakken bayani kan ibtila’in ba amma ya sanya gobarar a sahun hadurra mafiya tayar da hankali da kasar ta gamu da su a baya-bayan nan.

A cewar ministan cikin mutane 34 da suka mutu a gobarar har da kananan yara 2 yayin da wasu mutum 20 yanzu haka ke karbar kulawar gaggawa a asibiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.