Isa ga babban shafi

Benin ta fara daukar sabbin sojoji aiki don yaki a runduna ta musamman

A Jamhuriyar Benin, an fara daukar matasa aikin soji domin shiga runduna ta musamman da za ta yi yaki da ta’addanci mai dakaru dubu 5 da gwamnatin kasar ta sanar tun cikin watan Afrilun da ya gabata. 

Wasu dakarun Sojin Benin.
Wasu dakarun Sojin Benin. Reuters/Gonzalo Fuentes
Talla

Jamhuriyar Benin ta fara fuskantar hare-hare daga kungiyoyi masu dauke da makamai, tun a shekarar 2021, abin da ya sa shugaban kasar Patrice Tarlon ya kudiri kafa wata runduna ta musamman da za ta yaki ta’addanci a kan iyakokin kasar. 

Shi dai wannan tsarin na daukar sojoji an tsara shi ne a matakai daban-daban, kuma wanda aka fara yanzu, ya tanadi daukar matasa dubu 3 da 500 cikin har da masu kwarewa ta musamman a fannonin dogaro da kai, kamar kanikanci, direbobi, harkar gine-gine da sauransu. 

Daga cikin sharuddan zaben wadanda suka cancanci shiga aikin rundunar sojin ta musamman, dole ne ka kware da akalla ɗaya daga cikin harsunan da ake magana da su a kan iyakokin Benin da Burkina Faso. 

Yanzu haka dai matasan sun kammala jarrabawa a bangaren motsa jiki, kafin gwajin lafiyarsu a ranar 17 ga watan Yuni, wanda ke kawo karshen wa’adin daukar aikin. 

Daga nan ne za a horar da su har tsawon watanni shida daga masu bada horo na cikin gida, kafin daga bisani su samu kwarewa ta musamman daga masu bada woro daga kasashen Amurka da kuma Belgium.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.