Isa ga babban shafi

Makomar dimokuradiyya a Jamhuriyar Benin shekaru 2 bayan ci gaba da tsare 'yan adawa

Bayan kafuwar dimokuradiyya a shekarar 1991 tare da zaben Nicéphore Soglo a matsayin Shugaban kasa na farko, jamhuriyar Benin da ke kudu da hamadar Sahara ta samu shiga sahun kasashe da siyasa ta samu gindin zama shekaru 25.

Wani yanki na gundumar Tokpa a Cotonou, da ke Jamhuriyar Benin. 4 ga watan Maris, 2016.
Wani yanki na gundumar Tokpa a Cotonou, da ke Jamhuriyar Benin. 4 ga watan Maris, 2016. © REUTERS/Akintunde
Talla

A cikin 2016, abubuwa sun fara yin muni lokacin da Shugaba Talon, dan kasuwa mai shekara 63, ya karbi mulki. A shekara ta 2018,  gwamnatin sa ta bullo da sabbin dokoki masu tsauri.

 Hukumar zabe,wanda ta kumshi kawayen Shugaba Talon, ba tare da baiwa wakilan  jam'iyyun adawa damar shiga zaben 'yan majalisa na 2019 saboda zargin rashin bin doka.

Bayan hawansa karagar mulki, shugaba Talon ya daure mafi yawan abokan hamayyarsa ko kuma tilasta yin hijira zuwa kasashen waje(Sebastien Ajavon,Richard Boni Ouorou,Komi Kountche…..).

 Bugu da ƙari, ya ƙirƙiro Kotu ta musamman mai suna CRIET (Kotun da ke hukunta masu yiwa tattalin arziki zagon kasa da ta'addanci), Wanda a gaskiya shugaban kasa ne ke taimakawa  wajen gurfanar da abokan hamayyarsa na siyasa.

Wani alkali kotun da aka sani da (CRIET) da ya gudu daga kasar Benin ya bayyana haka a RFI (Radio France International), cewa Kotun tana karɓar "umarni" daga shugabannin siyasa na kasar.

Richard Boni Ouorou

A cikin hirarsa ta baya-bayan nan, masanin kimiyyar siyasa Richard Boni Ouorou ya nuna shakku kan yadda ake aiwatar da tsare-tsaren  kamar yadda shari'ar Jamhuriyar Benin ke yi. Wannan dan kasar Benin daga kasashen waje a fili ba ya da niyya ya ci gaba da kasancewa a bayan wannan tsari. Ta hanyar budaddiyar wasika, ya kalubalanci ’tsarin gudanar da shari’a,yadda ake amfani da wannan matakin shari’a na musamman.

Richard Boni Ouorou dan siyasa a Jamhuriyar Benin
Richard Boni Ouorou dan siyasa a Jamhuriyar Benin © Benin

A lokacin zaben shugaban kasa, an kame yan siyasa da dama a kasar ta Benin.Daga Janairu zuwa Satumba 2021, an kama mutane da dama  saboda dalilai ko manufofi na siyasa, yawancinsu suna ciki  jiran shari'a.

Fursunonin siyasa sun kasance a gidan yari na Cotonou, Parakou, Abomey da Akpro-Misserete.

Recky Madougou,'Yar siyasa bangaren adawa a jamhuriyar Benin
Recky Madougou,'Yar siyasa bangaren adawa a jamhuriyar Benin AFP - ERICK CHRISTIAN AHOUNOU

A wannan rana ta 03 ga watan Maris 2023,bikin tunawa da bakin ciki ga masu kare dimokuradiyya da 'yancin dan Adam,shekara biyu ke nan da aka kama Reckya Madougou.Kotun ta yanke mata hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari saboda samun ta da laifin aikata zagon kasa ga tattalin arziki da ta'addanci da hada baki da kungiyar masu aikata laifuka da ta'addanci, har yanzu tana tsare duk da bukatar a sake ta nan take a ranar 2 ga Nuwamba, 2022 da wata kungiyar daga Majalisar Dimkin Duniya ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.