Isa ga babban shafi

Jamhuriyar Benin ta kori wani dan kasar Belgium daga kasar

Kotu a  Jamhuriyar Benin ta ba da umarnin korar wani dan kasar Belgium da aka yanke masa hukunci a kasarsa a shekarar 2016 saboda  daukar nauyin masu ikirarin jihadi.

Harabar kotun hukunta ayyukan ta'addanci da yiwa tattalin arziki zagon kasa a Benin
Harabar kotun hukunta ayyukan ta'addanci da yiwa tattalin arziki zagon kasa a Benin AFP - YANICK FOLLY
Talla

 Jean-Louis Denis, wanda ake yi wa lakabi da "Denis The Submissive", dan kasar Belgium mai shekaru 49, an gabatar da shi a jiya juma’a ga mai gabatar da kara na musamman na kotun dake kula da harakokin ta’addanci da yiwa tattalin arziki zagon kasa da aka sani  da CRIET.

Alkali Mario Metonou ya bayar da umarnin a kore shi a yammacin ranar Juma'a, bisa la'akari da tarihinsa, wato hukuncin da alkalin kasar Belgium ya yi masa na tura matasa musulmi cikin sahun mayakan jihadi a kasar Syria.

Jean-Louis Denis ya isa Benin  a cikin jirgin kamfanin Ethiopian Airlines, yana da tikitin dawowa daga kamfanin.

Majiya daga kasar ta Benin ta ce "Denis The Submissive" ya bayyana a yayin sauraren karar da ya yi cewa ya zo kasar Benin ne don duba da kuma kafa wani babban aikin noma.

Har ma ya sami lokaci don ziyartar gidaje da yawa a Kétou a kudu, Dassa a tsakiya da Parakou a arewa.

Jami’na tsaro sun kama  shi ne a Tourou wanda ba shi da nisa da Parakou a arewacin kasar saboda gudun motar da ke dauke da shi. A lokacin da ya bayyana gaban álcali na CRIET,  Jean-Louis Denis ya kasa bayar da hujjar kudaden tallafin da ya ke da shi na aikin noma.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.