Isa ga babban shafi

Jamhuriyar Benin ta gargadi masu goyon bayan ayyukan ta'addanci

Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta yi kashedi a game da yadda masu ikirarin jihadi ke kokarin samun magoya baya a kasar, musamman a dai dai wannan lokaci da ‘yan bindigar ke tsananta kai hare-hare a arewacin kasar.

Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyyar Benin.
Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyyar Benin. AFP/File
Talla

Duk da cewa gwamnatin kasar na ci gaba da tura karin jami’an tsaro zuwa yankin arewa mai iyaka da Burkina Faso wanda ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, to amma mahukunta a birnin Cotonou na nuna fargaba a game da masu da’awar jihadin ke kokarin samun magoya baya a yankin.

Sanarwar da gwamnati ta fitar a wannan laraba, ta ce tabbas jami’an tsaro sun hallaka dimbin ‘yan ta’addar, to amma kuma akwai bayanan da ke nuni da cewa suna ci gaba da shiga cikin al’umma domin samun magoya ta hanyar yi masu alkawurra.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, daga cikin mutanen da suka amince su mara wa kungiyar baya, akwai wadanda ake cusa wa mummunar akida, yayin da ake bai wa sauran kwayoyi masu kawar da hankula domin afka wa jami’an tsaro, fararen hula da kuma wawashe dukiyoyinsu.

Gargadi na karshe da ke kunshe a sanarwar ta gwamnati, na cewa duk wanda aka samu da laifin kin bai wa jami’an tsaron kasar goyon baya a yankin da ke fama da ta’addanci, kai-tsaye ana kallonsa a matsayin mai mara wa ta’addanci baya, kuma zai fuskanci fushin hukuma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.