Gwamnatin Benin ta kwace illahirin kadarorin dan adawa Sebastien Ajavon
Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta kwace illahirin kadarorin jagoran ‘yan adawar kasar Sebastien Adjavon da ke gudun hijira a Faransa, bayan da kotu ta same da laifin kin biyan harajin da ya kai cfa milyan 160.
Wallafawa ranar:
A ranar 22 ga watan maris da ya gabata ne kotun koli ta tabbatar da samun dan adawar da wannan laifi, inda a karshen mako wakilin kotu da kuma jami’an tsaro suka shiga gidansa da ke birnin Kwatanu tare da kwashe illahirin kadarorinsu.
Lauyan jagoran yan adawan Jamhuriyar Benin Me Marc Bensimon ya bayyana takaicin sa ganin ta yada gwamantin kasar ta Benin ke yiwa jagoran yan adawa bita da kuli.
Tun a shekara ta 2017 ne Jagoran yan adawar kasar ta Benin,Sebastien Ajavon ke samu mafaka a Faransa.
Yan adawa na kalon Shugaban kasar Patrice Talon a matsayin dan kama karya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu