Isa ga babban shafi

Rundunar Sojin Benin ta dakile wani harin ta'addanci a Arewacin kasar

Rundunar sojin Jamhuriyar Benin ta yi nasarar dakile wani hari da ‘yan ta’adda suka shirya kai wa yankin arewa maso yammmacin kasar, wanda bayanai ke cewa 'yan ta'addan sun kitsa yadda za a kai harin ne daga makwabtan kasar wato Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso.

Wasu dakarun Sojin Benin.
Wasu dakarun Sojin Benin. wikimedia
Talla

Sanarwar da rundunar sojin ta Benin ta fitar ta ce yayin dakatar da harin dakarun soji sun yi nasarar hallaka ‘yan ta‘adda 8, yayinda da dama suka tsere da munanan raunuka.

Wasu alkaluma na nuni da cewa rundunar Sojin ta Benin ta yi nasarar dakile hare-haren ta'addanci har sau 12 daga bara zuwa yanzu, dai dai lokacin da barazanar tsaro ke ci gaba da tsananta a kasashen yankin Sahel sakamakon yadda kungiyoyin 'yan ta'adda masu alaka da Al Qaeda da kuma IS ke ci gaba da yawa bisa ikirarin aikata jihadi.

Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in yada Labarai na rundunar Sojin ta Benin, Ebnezer Honfonga ta ce da misalin karfe 12 na daren jiya ne sojojoji suka wargaza shirin ‘yan ta’adda na shiga kauyen Materi, da nufin kaddamar da jerin hare-hare.

Sai dai kuma bayan da rundunar Sojin ta samu bayanai sirri ne ta afka musu ta hanyar yi musu kwantan bauna, duk da dai sun yi yunkurin mayar da martani ta hanyar tashin bama bamai da harbe harbe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.