Isa ga babban shafi

Gobara ta kashe mutane fiye da 70 a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu

Akalla mutane 70 suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wata wuta da ta tashi a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu da sanyin safiyar yau Alhamis.

Ana fargabar karuwar adadin mutanen da suka mutu a gobarar ta birnin Johannesburg.
Ana fargabar karuwar adadin mutanen da suka mutu a gobarar ta birnin Johannesburg. AP
Talla

Jami’an kwana-kwana da suka kai daukin gaggawa a ginin da wutar ta tashi, sun ce zuwa yanzu an dauko gawarwakin mutane 73 sai kuma wasu mutane 43 da suka kone wadanda aka gaggauta mika su ga asibiti don ba su kulawa.

Kakakin Hukumar Daukin Gaggawa ta Birnin Johannesburg Robert Mulaudzi ya ce wutar ta tashi ne da safiyar yau Alhamis kuma kawo yanzu ba a kai ga gano musabbabinta ba.

A cewar jami’in, wutar ta barnata tarin dukiya lura da yadda ta tashi a rukunin gidaje masu tsayi da ke tsakar birnin baya ga mutane fiye da 200 da ta shafa.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa har zuwa yanzu, ana ci gaba da laluben wasu da suka bace kuma akwai yiwuwar samun karin gawarwaki lura da cewa ginin na kunshe da daruruwan mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.