Gobarar daji: Kimanin mutane dubu 30 ne aka umurta su bar yammacin Canada
Gobarar daajin da ta addabi yamacin Canada ta ta’azzara a jiya Lahadi, a yayin da aka yi ta kwashe mazauna yankunan da abin ya shafa daga gidajensu zuwa tudun mun-tsira.
Wallafawa ranar:
Wutan da ke ci gaba da ci ba kakkautawa, tana barazana ga dimbim yankuna a kwarin Okanagan, ciki har da birnin Kelowna, a yankin British Columbia.
Mahukuntan yankin sun bayyana lamarin a matsayin mai tayar da hankali, inda aka jiyo ministar kula da agajin gaggawa Bowinn Ma tana shawartar masu yawon bude ido da su guji zuwa inda gobarar ta shafa.
Kimanin mutane dubu 30 ne ake kwashewa zuwa tudun mun-tsira, a yayin da wasu karin dubu 36 ke cikin jiran umurnin arcewa.
dubban mutanen dake kewayen yankin, da kuma wasu a yammacin garin Kelowna sun baar gidajensu tuni, kuma suna zama a sansanoni da otel-otel ko kuma da ‘yan uwa da abokai, a yayin da a sauran biranen ake jira ko za a ji umurnin cewa kowa ya bar inda yake.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu