Isa ga babban shafi

Gobarar daji a yammacin Canada ta kara kamari - Hukumomi

Gobarar daji a lardin British Columbia da ke yammacin kasar Canada ta yi kamari a ranar Asabar, yayin da adadin mutanen da aka basu umarnin ficewa daga yankin ya rubanya, bayan da hukumomi suka yi gargadin kan tabarbarewar lamura nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

Yadda jami'an kashe gobara na faransa ke kokarin shawo kan wutar dajin da ke ci a kusa da Chibougamau a yankin Quebec na kasar Canada, ranar 18 ga watan Yunin 2023.
Yadda jami'an kashe gobara na faransa ke kokarin shawo kan wutar dajin da ke ci a kusa da Chibougamau a yankin Quebec na kasar Canada, ranar 18 ga watan Yunin 2023. © Public Safety Canada / AFP
Talla

Lardin ya ayyana dokar ta-baci a ranar Juma'a don samun damar shawo kan hadurran da ke da alaka da gobara, yayin da wutar da ba a iya sarrafa ta ta fara ruruwa a cikin British Columbia, abin da ya haifar da rufe wasu sassan wata babbar hanya tsakanin gabar tekun Pacific da sauran yammacin Kanada, bayan asarar dukiya da yawa da aka yi.

Halin da ake ciki a yanzu yana da muni," a cewar gwamnan yankin Daniel Eby ga manema labarai, yana mai cewa kimanin mutane 35,000 ne ake kokarin kwashewa, sannan wasu 30,000 suna jiran tsammani.

Eby ya ce lardin na matukar bukatar matsuguni ga masu gudun hijira da masu kashe gobara tare da ba da umarnin hana tafiye-tafiye marasa mahimmanci don samar da wuraren kwana na wucin gadi.

Hukumomi sun kuma bukaci mazauna yankin da su guji yin amfani da jirage marasa matuka a yankin da ke fama da gobarar, suna masu cewa hakan na iya kawo cikas ga yunkurin kashe gobara.

Wutar dai tana ci gaba da ci ne a kusa da Kelowna, wani birni mai tazarar kilomita 300  gabas da Vancouver, mai yawan jama'a kusan 150,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.