Isa ga babban shafi

Canada ta gayyaci masu sana'o'in hannu daga Afrika don basu guraben aiki

Canada ta kaddamar da wani sabon tsarin bayar da mafaka ga ‘yan ciranin Afrika inda ta gayyaci kwararru a fannonin aikin hannu daga Najeriya da sauran kasashen nahiyar don ba su guraben aikin yi, karkashin shirin da ke da nufin bunkasa tattalin arzikin kasar ta nahiyar Amurka.

Cikin nau'in masu sana'o'in da Canada ke nema har da Kafintoci da Plumba da kuma masu walda.
Cikin nau'in masu sana'o'in da Canada ke nema har da Kafintoci da Plumba da kuma masu walda. RFI/Laura Angela Bagnetto
Talla

Wata sanarwa da hukumar kula da ‘yan cirani da bakin haure da kuma bayar katin dan kasa ta Canada ta fitar a makon nan, ta ce ta na bukatar kwararru a fannin kafinta da walda da kuma gyaran famfo don samun guraben ayyukan yi a kasar ta nahiyar Amurka.

A cewar sanarwar tsarin bayar da izinin shiga kasar ta Canada zai fifita kwararru a fannonin aikin hannu fiye da wadanda basu da kwarewa kuma suke neman damar shiga kasar.

Baya ga wadannan fannoni da Canada ke neman kwararru daga kasashen na Afrika wanda ta kama sunan Najeriya a farko, akwai kuma masu gogewa ta musamman a fannonin kasuwanci da ta bukata baya ga duk wani nau’in ayyukan hannu ko na karfi, a yunkurin da kasar ke yi na samun kwararrun da za su taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasar.

Wannan yunkuri na karkashin kudirin da gwamnatin ta Canada ta gabatar da ke na bayar da izinin zama ga baki ‘yan gudun hijira akalla dubu 500 duk shekara har zuwa nan da shekarar 2025 wanda ke nuna za ta karbi ‘yan cirani miliyan 1 da dubu 500 nan da shekaru 3.

A 2022 kadai Canada ta bayar da izinin zama na dindindin ga baki dubu 437 da 120 kusan karin kashi 8 idan na kwatanta da adadin da ta baiwa a 2021.

Cikin wannan alkaluma na bakin a Canada kuwa har da ‘yan Najeriya wadanda yawansu ya karu daga mutum dubu 15 da 595 a 2021 zuwa dubu 22 da 130 a 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.