Isa ga babban shafi

Za a sake gina katafaren filin wasannin Olembe a birnin Yaoundé

Gwamnatin Kamaru da kamfanin Canada da ke da alhakin gina wani katafaren filin wasanni a birnin Yaoundé sun sanar a yau Juma'a cewa za a sake fara aiki a wannan wurin, wanda ya katse a shekarar da ta gabata bayan takaddama tsakanin bangarorin biyu.

Filin wasa na Olembe na Yaounde a kasar Kamaru
Filin wasa na Olembe na Yaounde a kasar Kamaru Pierre RENE-WORMS / FMM - PIERRE RENE-WORMS
Talla

A ranar Larabar da ta gabata, kamfanin, Magil Construction Corporation, ya yi tir da tsokacin ma'aikatar wasannin kasar, wanda ya zarge shi a cikin wata wasika na cikin gida da ya so ya soke kwangilarsa ba tare da izini ba. Kamfanin, wani reshen kungiyar Fayolle na Faransa, a nasa bangaren, ya zargi gwamnatin kasar ta Kamaru da kin biyan kudaden ta tun watan Yulin 2021.

An katse aikin a watan Agustan da ya gabata na wata guda, sannan ya ci gaba da aiki a cikin mafi ƙarancin yanayi na rashin kudi har zuwa yau , in ji kamfanin na Canada ga AFP.

A gefen ziyarar da ya kai wurin a yau Juma'a, Ministan wasanni na Kamaru, Narcisse Mouelle Kombi, ya jaddada burin gwamnatinsa na ganin wannan aikin ya yi nasara gaba daya kuma Magil ya koma bakin aiki cikin sauri.

 An sami "babban rashin fahimta" kuma "za a ci gaba da gine-ginen", a nasa bangaren ya tabbatar wa mataimakin shugaban kamfanin na Canada, Franck Mathière, wanda  ya kasance a wannan ziyara tare da kara  cewa  wannan aikin zai zo karshe, alkawari ne da aka sabunta tsakanin gwamnati da Magil.

Magil ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa yana fatan komawa bakin aiki a ranar Litinin 16 ga watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.