Isa ga babban shafi

Qatar 2022: Ghana da Kamaru zasu san matsayinsu yau

Spain ta tsallaka zuwa zagayen 'yan 16 na gasar cin kofin duniya duk da rashin nasara da ta yi a hannun Japan wacce ta bada mamaki tare da jagoranci rukunin E da ci 2-1, a daren Alhamis, inda aka fitar da Jamus da ta taba lashe kofin sau hudu duk da nasarar doke Costa Rica da ci 4 - 2.

'Yan wasan tawagar Kamaru yayin wasansu da Serbia a gasar cin kofin duniya na Qatar 2022
'Yan wasan tawagar Kamaru yayin wasansu da Serbia a gasar cin kofin duniya na Qatar 2022 REUTERS - CARL RECINE
Talla

Spain da Jamus dai sun kare ne da maki hudu kowanne, amma Spain ta samu nasarar zuwa zagayen na biyu da yawan kwallaye.

Da wannan nasara Spain za ta kara ne da Morocco a zagayen ‘yan 16, yayin da Japan za ta kara da Croatia.

Morocco ta samu gurbin ne bayan doke Canada da ci 2-1 a wasan da suka fafata jiya, inda ta zama ta 1 a rukunin ‘F ‘ da maki 7, wanda shine karon farko cikin shekaru 36, Morocco ta tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar kofin duniya.

Belgium ta fice daga gasar

Itama Belgium ta kawo karshen halartan gasar cin kofin duniya a Qatar bayan da suka tashi babu ci da Croatia, dama tana neman dole sai ta yi nasara a wasan na jiya kafin samun damar zuwa zagaye na biyu, yanzu Croatia ce zata hadu da Japan a siri daya kwalle.

Za'a kawo karshen wasannin rukuni

A wannan Jumma'a za’a Karkare wasannin rukuni, inda rukunin ‘G’ da ‘H’ zasu doka ciki harda kasashen Afirka biyu wato Ghana da Kamaru.

A rukunin ‘G’ Brazil ce kawai ta haye zagaye na biyu, Switzerland da Kamaru da Sabia duk na neman nasara a wasannin da zasu fafata.

A rukunin ‘H’ ma Portugal ce kawai ta kai zagaye na biyu, Ghana da Koriya da Uruguay duk suna bukatar lashe haduwar da zasu yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.