Isa ga babban shafi

Morocco ta lallasa Belgium a gasar cin kofin duniya

Kasar Morocco ta samu gagarumar nasara akan Belgium a gasar cin kofin duniya dake gudana a Qatar, inda ta doke ta da ci 2-0 a karawar da suka yi yau Lahadi.

Yadda wasa ya wakana tsakanin Morocco da Belgium
Yadda wasa ya wakana tsakanin Morocco da Belgium REUTERS - AMR ABDALLAH DALSH
Talla

Abdelhamid Sebri ya jefawa Morocco kwallon ta na farko a minti 73 da fara wasan, yayin da zakaria Aboukklal ya jefa kwallo ta biyu a minti 93, abinda ya baiwa kasar nasara da kuma hawan teburin rukuni na 6 da maki 4, yayin da Belgium ta koma matsayi na biyu da maki 3.

Wannan gagarumar nasara ta farantawa 'yan Afirka rai, lura da cewar har yanzu kasashen dake wakiltar nahiyar basu samu nasara ba, baya ga nasarar Senegal, yayin da Belguim ke mataki na 4 na kasashen da suka fi iya kwallo a dunia.

Yanzu haka ana karawa tsakanin Croatia da Canada wadanda suma suke cikin wannan rukuni na gasar, yayin da Croatia ke da mati guda, ita kuwa Canada bata da maki.

A karawar da aka yi da safe, Costa Rica ta doke Japan da ci 1-0, yayin da anjima da karfe 8 Spain zata fafata da Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.