Isa ga babban shafi

Sama da mutum 1000 ne suka bace a gobarar Maui

Akalla mutane  dubu 1 da 100 ne har yanzu ba a gan su ba makonni biyu bayan wata mummunar gobarar dajin da ta barke a tsibirin Maui na Hawaii, kamar yadda hukumomi suka tabbatar a ranar Talata, inda hukumar FBI ke neman taimakon ‘yan uwa wajen gano gawarwakin mamatan.

Gidaje da dama gobarar dajin ta lakume a Lahaina, Hawaii, ranar Laraba, 16 ga Agusta, 2023.
Gidaje da dama gobarar dajin ta lakume a Lahaina, Hawaii, ranar Laraba, 16 ga Agusta, 2023. © Jae C. Hong / AP
Talla

Gobarar ita ce mafi muni da ta afku a Amurka cikin karni guda, inda ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 115, bisa ga adadin wucin gadi da hukumomi suka tattara.

Kungiyoyi daban-daban da suka hada da Red Cross har ma da jami'an 'yan sanda sun wallafa sunayen mutanen da ake neman su.

A yanzu  Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) tana kokarin tattarawa tare da tantance bayanai, kamar yadda  wakilinta na musamman Steven Merrill  ya bayyana ga manema labarai a ranar Talata.

Muna binciken jerin sunayen da muke da su domin mu iya tantance wanda a zahiri har yanzu ba a san inda suke ba, in ji Merrill.

Ya kara da cewa, ya zuwa ranar Talata, hukumar ta FBI ta kirga mutane 1,100 da suka bace, kuma adadin zai iya karuwa nan gaba.

Shugaban 'Yan sandan Maui, John Pelletier ya ce hukumomi na tace bayanan kuma suna fatan tantance jerin mutanen da suka bata a cikin 'yan kwanaki masu zuwa..

Jami'an FBI sun kuma tattara samfuran gwajin kwayoyin halitta na DNA daga iyalan wadanda suka bata musamma wadanda ba za su iya zuwa Maui ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.