Isa ga babban shafi

Masu aikin ceto na kokarin shawo kan wutar dajin Maui yayinda mutum 55 suka mutu

Gobarar daji ta Maui ta kashe akalla mutane 55, adadin da ake sa ran zai karu, da kuma barna a wuraren shakatawa na Lahaina da zai dauki shekaru masu yawa da biliyoyin daloli kafin a sake gina shi, in ji hukumomin Hawaii da ke Yammacin Amurka.

Yadda gobarar dajin Maui ta mamaye cocin Waiola mai cike da tarihi a Lahaina.
Yadda gobarar dajin Maui ta mamaye cocin Waiola mai cike da tarihi a Lahaina. © AP / Matthew Thayer
Talla

Gwamna Josh Green ya ce gobarar da ta mayar da da yawa daga cikin Lahaina zuwa ga tururin hayaki, ita ce bala'i mafi muni a tarihin jihar, wanda ya sa dubban mutane suka rasa matsuguni tare da daidaita gine-gine da suka kai 1,000.

Guguwar mai saurin tashi, wacce ta fara a ranar Talata, ta bazu a wajen garin, ta kuma abkawa birnin Lahaina mai tarihi wanda ya taba zama babban birnin Masarautar Hawai.

"Kada wanda ya je garin Lahaina," a cewar sakon da hukumar gudanarwar gundumar yankin ta wallafa a shafin Tweeter, sa'o'i kafin a rufe dukkan hanyoyin shiga da wajen Maui, sai jami'an hukumar bada agajin gaggawa kadai da aka sahalewa shiga.

Bayanai na cewa yanzu haka, fiye da mutane 2,100 ne suka kwana a cibiyoyin da aka kebancewa wadanda ibtila'in ya rutsa da su.

Gobarar Hawaii ba kamar yawancin wadanda ke faruwa bane a Yammacin Amurka. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.