Isa ga babban shafi

Ambaliya da zaftarewar kasa ta tilasta rufe makarantu a California

Hukumomi da al’ummar kudancin jihar California ta kasar Amurka  sun tashi da sharar tabo  bayan da ruwan sama mai kama da bakin kwarya da aka kwarara a yankin ya haddasa zaftarewar kasa  da ambaliyar ruwa da tabo, lamarin da ya tilasta rufe makarantu da kasuwanni a Litinin din nan. 

Wani sashe na yankin  Palm Springs, a yaayin da guguwar 
 Hilary taa isa California.
Wani sashe na yankin Palm Springs, a yaayin da guguwar Hilary taa isa California. REUTERS - ALAN DEVALL
Talla

A wasu sassan wannan yankin, an samu  saukar ruwan sama da  ya kai inci 11, daidai da centimeter 28, san nan daga bisani mahaukaciyar guguwar nan ta Hilary ta ratsa ilahirin yankin. 

A yankin Oak Glen, wanda ke gefen tsauni, tsakanin Los Angeles da Palm Springs, tabo daga zaftarewar kasa da aka samu ne ya mamaye unguwanni, a yayin da ake iya ganin ma’aikata suna katsar tabo da shebur, tare da kokarin  ceto wadanda ambaliyar tabo  ta yi wa kofar raggo. 

Wannan lamari ya sa an jinkirta bude makarantu da kwana guda a gundumomi da dama ciki har da Los Angeles, bayan hutun karshen zangon karatu da aka yi.  

Mahukunta sun bude mafaka na dimbim jama’a har guda  biyar, suka kuma sanya jami’ai guda  dubu 7 da dari 5, cikinsu har da dakarun tsaron kasa na National Guards, da kuma tawagar ceto ta cikin ruwa,  kamar yadda gwamnan California Gavin Newsome ya  bayyana. 

Masana kimiyya sun yi kashedin cewa mahaukatan guguwa da ambaliya na dada yin karfi a yayin da duniyar ke kara zafi sakamakon sauyin yanayi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.