Adadin wadanda suka mutu sakamakon gobarar Hawaii ya kai 93
A kalla mutane 93 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon gobarar dajin da ta mamaye kauyen Maui, dake kan tsibirin Hawai na kasar Amurka, kamar yadda sabon sakamakon iftila’in ya nuna.
Wallafawa ranar:
A ranar Asabar, mazauna yankin Maui, sun bayyana Iftila’in da zama mafi muni a kan manda ya taba faruwa a yankin kasar Amruka, inda tsibirin na Hawai ya fuskanci ambaliyar tsunami, da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 61 a 1960
Yanzu haka dai bayan lafawar wutar, mazauna garin Lahaina, mai kunshe da kimanin mutane dubu 13.000 sun fara nazarta irin barnar da wutar dajin ta yi masu, inda ta barsu hannu rabbana, ba komai sai rayukansu.
Anthony Garcia, wani tsoho ne mai shekaru 80 a duniya, ya bayyana matukar damuwarsa, bayan ya rasa komai, a garin da ya tare yau sama da shekaru 30 da suka gabata.
Mutanen da suka tsira da rayukansu daga iftila’in na ci gaba da bincikar gawawakin da wutar ta lakume, bisa zummar samun hotunansu
Duk inda ka duba, gabarar ta lashe gidaje da gonaki musaman a katafaren dajin gonakin ayaba, da ke jawo masu yawon buda ido, wadanda yanzu haka gobarar ta lashe, kamar ba a taba yin su ba.
Kamar dai mazauna tsibirin, yanzu haka kotu ta bayyana buda soma binciken shara’a, domin gano dalilin da ya sa wutar ta yi kamarin, binciken da ya karkata kan yadda mahukumta suka gudanar da ayukan agajin gaggawa a lokacin gobarar. Yadda ayukan sadarwa suka gudana a lokacin iftila’in na daga cikin abubuwan da ake dora almar tambaya a Kansu.
Mazauna yankin sun sanar da AFP cewa, sun yi amfani ne da tsohuwar hanyar sadarwa, daga wannan ita ciyar kwakwa zuwa wacan, ma’ana daga baki zuwa kunne.
Uwargida Vilma Reed, ta bayyana cewa, ita bata hangi wutarba sai bayan da ta zo daf da kofar gidanta da wutar ta lakume.
Garin Maui dai, ya fuskanci katsewar wutar lantarki a lokacin gobarar, wanda ya sa lambar layin wayar gaggawa 911 ta daina aiki a wasu yankuna na Tsibirin, a yayin da kuma aka ce, ba a kunna jiniyar gargadin tashin gobara ba a lokacin faruwar iftila’in.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu