Isa ga babban shafi
RAHOTO

Gwamnatin Kamaru ta tsaurara dokar kayyade farashin kayayyaki

Matakan da gwamnatin Kamaru ke dauka wajen kayyade farashin kayan masarufi da kuma tabbatar da cewar ‘yan kasuwa ba suyi amfani da damar da suke da ita na kara yawan farashin kayyaki ba na matukar tasiri wajen hana hauhawan farashin kayan abinci a kasar. 

Gwamnatin kasar ta ce za a dauki mataki mai tsauri kan 'yan kasuwar da aka samu da tsawwala farashin kayayyaki.
Gwamnatin kasar ta ce za a dauki mataki mai tsauri kan 'yan kasuwar da aka samu da tsawwala farashin kayayyaki. © MDPI
Talla

A shekarar 2022 ne aka samu karuwar farashin alkama a kasar da ke tsakiyar Afirka, abin da ya sanya kungiyar dillalan hatsi suka dakatar da shigar da ita, domin nemarwa kan su mafita game da tsadar ta.

A watan Maris din shekarar 2023 ne, dubban mata a kasar suka fito zanga-zangar bayyana damuwarsu kan yadda farashin kaya da tsadar rayuwa ke karuwa a kasar, inda suka dora alhakin hauhawar farashin kaya da kuma makamashi akan gwamnati da kuma mamayar da Rasha ta yi a Ukraine.

Cikin shekarar 2022 ne, shugaban kasar Paul Biya ya bayar da umarnin raba tallafin dala miliyan 15 domin gudanar da noman alkama da kuma shinkafa, domin tunkarar karancin abinci da ke neman jefa kasar cikin yunwa.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Lourwanou Ousmanou.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.