Isa ga babban shafi

Kamaru na neman taimakon Amurka don biyan bashinta

Gwamnatin Kamaru ta ce tana tattaunawa da Amurka domin maida ta cikin yarjejeniyar kasuwanci ta AGOA domin taimaka wa shirinta na habbaka hanyoyoyin samun kudaden shiga daga ketare, a wani mataki na dakile matsalar basussuka da suka yi mata katutu. 

Shugaban Kamaru Paul Biya
Shugaban Kamaru Paul Biya Getty Images via AFP - KEVIN DIETSCH
Talla

Ministan Tattalin Arzikin kasar Kamaru Alamine Ousmane Mey ya bayyana hakan yayin wani taron da Cibiyar Bincike ta Atlantic Council ta shirya a gefen taron Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF da Bankin Duniya a birnin Washington na kasar Amurka. 

Mista Mey ya ce, kasarsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta sauke dumbin basukan da ke kanta ta hanyar bunkasa hanyoyin samun kudin shigar da take samu daga kasashen waje. 

Kuma domin cimma wannan burin, kasar za ta sake tattaunawa da Amurka domin kawo karshen janye ta da ta yi daga cikin yarjeniyar kasuwancin Washington ta Afirka ta AGOA, wanda ke bai wa kasashen Afirka da suka cancanci shiga kasuwannin Amurka ba tare da biyan haraji ba. 

Minisatan na bugun kirji ne bayan da IMF ya bayyana kasar Kamaru a matsayin wanda ke cikin hadarin fuskantar matsalar bashi. 

Koda yake a rahotansa na baya-bayan nan, Asusun Bada Lamuni na Duniya ya yi hasashen cewa kasar Kamaru, mai arzikin mai a Afirka ta Tsakiya, za ta samu ci gaban tattalin arziki da kashi 4.3% a bana bayan da ta fuskanci kashi 0.5% a shekarar 2020. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.