Isa ga babban shafi

Faransa ta dakatar da bayar da visa a kasashen Nijar, Burkina Faso da Mali

Faransa ta ce ta daina bayar da takardar visa a ofisoshin jakadancinta da ke kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar, tare da dakatar da duk wasu ayyuka da suka shafi musayar al’adu a tsakaninta da wadannan kasashe.  

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Tuni dai wannan mataki ya samu mummunar suka daga kungiyoyi da kuma masu ruwa da tsaki a lamurran da suka shafi yada al’adu daga sassan duniya ba wai a cikin wadannan kasashe uku da abin ya shafa kawai ba. 

A cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar, matakin daina bayar da visa da kuma daina musayar al’adu a tsakanin Faransa da kasashen, ya fara aiki ne tun ranar 7 ga wannan wata, to sai dai hakan bai shafi wadanda suka mallaki takardunsu na visa kafin ranar ta 7 ga wata da aka dauki matakin ba. 

Tuni ma’aikatar harkokin wajen ta sanar da kungiyoyi daban daban da suka kunshi mutanen da ke da kwarewa a fagen musayar al’adu a cikin Faransa, ta hanyar rubuta musu wasika don sanar da su a hukumance. 

A ranar 29 ga wata yulin da ya gabata ne Faransa ta sanar da dakatar da duk wani taimako da ta ke bai wa Jamhuriyar Nijar, yayin da ta dauki irin wannan mataki kan Burkina Faso a ranar 4 ga watan Agustan da ya gabata. 

Alaka tsakanin Burkina, Mali, Nijar da kuma Faransa, ta yi tsami ne sakamakon juyin mulkin da aka yi a kasashen uku da ke yankin Sahel. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.