Isa ga babban shafi

Sojojin Nijar sun saki bafaranshen da suka kama bayan kiraye-kirayen Faransa

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da cewa Sojojin da ke mulki a Nijar sun saki bafaranshen da suka kame tsawon makwanni.

Jagoran mulkin Sojin Nijar.
Jagoran mulkin Sojin Nijar. © Stringer / Reuters
Talla

Sakin na Stephane Jullien a yau alhamis na zuwa ne bayan kiraye-kirayen Faransa da kungiyar Tarayyar Turai na ganin lallai sojojin sun sake shi cikin gaggawa.

Sanarwar da ma’aikatar wajen ta Faransa ta fitar da safiyar yau alhamis ta ce, ta na maraba da matakin sakin Jullien  

Jullien, dan kasuwa da shafe tsawon lokaci a Nijar na taka muhimmiyar rawa wajen kare manufofin Faransa a kasar baya ga aikin wucin gadi a ofishin jakadancin da ke birnin Yamai.

Tun a ranar 8 ga watan Satumba ne Sojojin na Nijar suka kame Jullien biyo bayan tabarbarewar alaka tsakanin kasar ta yankin Sahel da Faransa wadda ta yi mata mulkin mallaka.

A talatar da ta gabata ne, Faransa ta bukaci gaggauta sakin Jullien tare da bayyana ci gaba da tsare shi a matsayin abin da ya sabawa doka.

A ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata ne Sojoji suka yi juyin mulki a kasar ta Nijar lamarin da ya kawo karshen mulkin Mohamed Bazoum tare da haddasa cikas ga manufofin Faransa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.