Isa ga babban shafi

Ba ma gaba da Faransa don mun bukaci ta fice a Burkina Faso - Traore

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Captain Ibrahim Traore ya ce kasar ba makiyiyar Faransa ba ce, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar kusan shekaru biyu da suka gabata.

Shugaban gwamnatin rikon kwarya na Burkina Faso kenan, 
 Kyaftin Ibrahim Traore.
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na Burkina Faso kenan, Kyaftin Ibrahim Traore. © Alexander Ryumin, Tass / Reuters
Talla

Shugaban wanda ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a gidan talibijin din kasar, ya ce matakin da gwamnatin soji ta dauka na neman ficewar sojojin faransa, ba wai yana nufin tana gaba da kasar bane.

Kyaftin Ibrahim Traore wanda ya dare karagar mulki kusan shekara guda da ta wuce ta hanyar juyin mulki, ya kuma nuna shakku kan tasirin kasancewar sojojin Faransa a Burkina Faso a wani bangare na yaki da masu tayar da kayar baya, wanda ya bukaci ficewar su a watan Janairu.

Tawagar Rasha ta tattauna da Kyaftin Traore a makon da ya gabata a birnin Ouagadougou kan batutuwan ci gaba da hadin gwiwar soji sannan Kyaftin din ya halarci taron da Rasha ta shirya da kasashen Afirka, da ya gudana a Saint Petersburg a watan Yuli.

Shugaban na gwamnatin sojin Burkina Faso dai, ya jaddada goyon bayan kasarsa ga Nijar, inda aka yi juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.