Isa ga babban shafi

'Yan adawan Tsakiyar Afirka na nisanta kansu daga masu ra'ayin sabon kudin tsarin mulki

A Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, kimanin mutane 2,000 zuwa 3,000 ne suka fito jiya juma’a a Bangui, babban birnin kasar, domin nuna goyon bayansu ga tsarin sauya kundin tsarin mulkin kasar, wanda za ya bai wa shugaban kasar Faustin Archange Touadéra yin tazzarce a shugabancin wannan kasa. 

 Faustin-Archange Touadéra,Shugaban kasar Afirka ta Tsakiya
Faustin-Archange Touadéra,Shugaban kasar Afirka ta Tsakiya © Barbara Debout / AFP
Talla

Jama’a sun taru  filin wasan Barthélémy Boganda dake babban birnin Bangui,taron da ake kalo a matsayin wani share fage na kada kuri'aa zaben na gobe lahadi, a wannan kasa da har yanzu ke fama da tawaye bayan shekaru na yakin basasa. 

Masu goyan bayan tazzarce a Tsakiyar Afirka
Masu goyan bayan tazzarce a Tsakiyar Afirka REUTERS - LEGER SERGE KOKPAKPA

Taron ya samu halartar Firaminista Félix Moloua, da Simplice Mathieu Sarandji, shugaban majalisar dokokin kasar. 

A kasar da kashi 71% na al'umma ke rayuwa kasa da kangin talauci a cewar bankin duniya, manyan jam'iyyun adawa da kungiyoyin farar hula gami da kungiyoyin 'yan tawaye masu dauke da makamai, sun yi kira ga jama’a da su kauracewa zaben rabba gardama.

 

Masu adawa da tasrin tazzarce na Shugaban Tsakiyar Afirka
Masu adawa da tasrin tazzarce na Shugaban Tsakiyar Afirka AFP - BARBARA DEBOUT

Sabon kundin tsarin mulkin wanda musamman ya tsawaita wa'adin mulkin shugaban kasa daga shekaru biyar zuwa bakwai tare da cire wa'adin mulki.

 

 

  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.