Isa ga babban shafi

Tsohon Fira Ministan Burundi ya shiga hannu bayan shafe kwanaki ana farautarsa

Jami’an tsaron Burundi sun cafke tsohon Fira Ministan kasar Alain-Guillaumme Bunyoni, watanni bakwai bayan korar shi daga mukamin nasa da shugaba Evariste Ndayishimiye yayi a watan Satumban shekarar 2022.

Jami'an tsaron kasar Burundi.
Jami'an tsaron kasar Burundi. AFP - ONESPHORE NIBIGIRA
Talla

Kafin sauke shi daga Fira Minista, Bunyoni ya rike mukamin babban sifeton ‘yan sandan Burundi.

Ministan tsaron cikin gidan kasar Gervais Ndirakobuca ne ya maye maye gurbin Bunyoni, kwanaki kalilan bayan da yayi gargadin cewar akwai yiwuwar a yi wa shugaba Ndayishimiye juyin mulki.

Jami’an ‘yan sanda da na leken asiri sun gudanar da bincike kan kadarorin Bunyoni guda uku a ranar Litinin ta makon jiya ba tare da gano inda yake ba.

Kafin shiga hannun da yayi, sai da jami’an tsaro suka shafe kwanaki suna nemansa ruwa a jallo, abinda ya sanya ko a makon jiya sai da suka kai samame daya daga cikin gidajensa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.