Isa ga babban shafi

Shugaban Burundi ya nada sabon Firaminista bayan gargadin juyin mulki

Shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye ya maye gurbin firaministansa da kuma babban mai taimaka masa a wani babban mataki na share fagen siyasa, bayan ya yi gargadin shirin "juyin mulki" ga gwamnatinsa.

Gervais Ndirakobuca
Gervais Ndirakobuca AFP
Talla

An rantsar da ministan tsaro Gervais Ndirakobuca a gaban majalisar dokokin kasar a matsayin sabon firaministan.

Sabon firaministan ya gaji Alain-Guillaume Bunyoni, wanda aka kora tare da babban hafsan farar hula na Ndayishimiye Janar Gabriel Nizigama a wani gagarumin sauyi na farko da aka yi a sama tun bayan hawan shugaban kasa shekaru biyu kadan da suka wuce.

Ndayishimiye, mai shekaru 54, tsohon Janar din soji, bai bayyana dalilan korar Bunyoni ba, amma a makon da ya gabata ya yi gargadin yunkurin juyin mulkin da aka yi wa gwamnatinsa.

Ba a dai san makomar Bunyoni ba, wanda ya kasance tsohon shugaban 'yan sanda kuma ministan tsaro da ya dade yana rike da mukamin jigo a jam'iyyar CNDD-FDD mai mulki.

Ndirakobuca, mai shekaru 52, na daga cikin jami'an kasar Burundi da ake zargi da haddasa tashe-tashen hankula a kan 'yan adawar gwamnati a wani kazamin rikici da ya barke a shekarar 2015, kuma yana ci gaba da kasancewa karkashin takunkumin EU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.