Isa ga babban shafi

Shugabannin kasashen gabashin Afirka sun fara taro a kan rikicin DR Congo

Shugabannin kasashen gabashin Afrika 7 za su fara wani taro yau Litinin, don tattauna batun matsalar tsaron da jamhuriyar demokradiyyar congo ke fuskanta, da kuma takun sakar da ke tsakaninta da Rwanda, lamarin da ke iya shafar sauran kasashen makwabta.

Shugbannin. kasashen gabashin Afrika a yayin taronsu a Dar es Salaam na Tanzania  31 ga watan Mayui 2015.
Shugbannin. kasashen gabashin Afrika a yayin taronsu a Dar es Salaam na Tanzania 31 ga watan Mayui 2015. AFP PHOTO / STRINGER
Talla

Tun a yammacin jiya Lahadi ne fadar shugaban kasar Kenya ta sanar da batun zaman taron na yau a Nairobi, wanda ta ce zai lalubo mafita don warware rikicin da Congo ke fama da shi tsawon shekaru.

Taron shugabannin kasashen na gabashin Afrika 7 na zuwa a daidai lokacin da rikici ke tsananta tsakanin kasar ta jamhuriyyar Congo da makwabciyarta Rwanda saboda yadda Kinshasa ke zargin Kigali da daukar nauyin ‘yan tawayen M23 da ke zafafa hare-hare a sassan kasar.

Sai dai Rwanda na ci gaba da musanta zargin da Congo ke mata yayin da da dukkaninsu ke zargin juna da kaddamar da hare-hare cikin yankunan juna ba baya wuce gona da iri a al’amuran cikin gida.

Sanarwar taron ta ruwaito shugaba Uhuru Kenyatta na kenya na cewa al’ummar Congo sun shafe tsawon lokaci suna wahaltuwa daga tashe-tashen hankula da ke haddasa asarar dimbin rayuka, wanda ke nuna bukatar da ke akwai ta dawwamar da zaman lafiya a kasar.

Ko a larabar makon jiya, sai da Kenyatta ya bukaci girke dakarun EAC a gabashin Congo don tabbatar da zaman lafiya, yayinda shugaba Felix Tshisekedi ke cewa Rwanda na son amfani da matsalar tsaron don mamaye wani yanki na Congo mai tarin albarkatun karkashin kasa ciki har da zinare da karafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.